11 Mayu 2020 - 05:45
Tashin Nakiya Ya Yi Ajalin Sojin Chadi Uku A Mali

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a kasar Mali, ta sanar da mutuwar sojojin kasar Chadi uku, bayan da motocinsu biyu suka taka nakiya a arewacin kasar Mali.

(ABNA24.com) Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a kasar Mali, ta sanar da mutuwar sojojin kasar Chadi uku, bayan da motocinsu biyu suka taka nakiya a arewacin kasar Mali.

Lamarin dai ya faru ne jiya Lahadi, a yankin Aguelok a cerwa tawagar ta (Minusma).

Ko baya ga sojojin da suka rasa ransu da akwai wasu hudu da suka samu munannen raunuka.

Babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya yi tir da allawadai da lamarin, yana mai shan alwashin gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyan aikin.


/129